Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta ce ba za ta wa jam’iyyun siyasa damar binciken sashen adana bayanan sakamakon zaɓen hukumar ba.

Shugaban kwamitin wayar da kan jama’a a kan alamuran zaɓe Festus Okoye ne ya shaida haka yayin tattaunawa da shi a vgidan talabiji na Channels.
Ya ce jam’iyyun ba su da damar binciken rumbun adana bayanan sakamakon zaɓen da aka yi domin an ba su kwafin sakamakon bayan sun sanya hannu.

Okoye ya ƙara da cewa, za su tabbata sun kammala aikin sabunta na’urar tantace masu kaɗa ƙuri’a zuwa ranar Talata domin aike da su zuwa rumfunan zaɓe.

Sannan sun shirya fuskantar dukkan ƙalubalen da ka iya zuwa yayin zaɓen gwamnoni da ke tafe.
Yayin da yake mayar da martani dangane da damar yin zaɓe ga masu katin zaɓe na wucin gadi, Okoye ya ce takardar da aka bai wa mutanen an ba su ne domin su san wajen da za su karɓi katin zaɓensu yayin da cikakken bayani ke ƙunshe a katin zaɓe na din-din-din.