Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta tabbatar da cewar za ta tabbatar ta gaggauta bayar da bayanan da jam”iyyar Labour party ta buƙata kamar yadda Shari’a ta bayar da dama.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana haka yau yayin da ya karbi tawagar lauyoyin jamiyyar a helkwatar hukumar.
Ya ce a halin da ake ciki su na ganawa da kwamishinonin zaɓe na jihohi domin duba yadda za su bayar da dukkan bayanan da su ka buƙata cikin hanzari.

Kuma ya ce za su yi hakan kamar yadda su ka sa a gaba.
