Gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagoranci mallam Nasir Ahmad El’Rufa’i ta gano shirin waasu yan siyasar jihar na tada zaune tsaye da sunan zanga-zanga.

Kwashinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Arwan shine ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau allhamis.

Arwan ya ja hankain Iyaye da sarakuna da su tsawatar wa da al’ummarsu domin kuwa duk wanda aka samu da laifi ba shakka sai doka ta hukuntashi.

ya cigaba da cewa gwamnati ba za ta bari wasu su ta da hankalin al’umma ba da sunan zanga zanga.

Samuel Arwan ya jajjada cewa babu wanda doka zata kyale matukar zai ba da gudunmawa wajen barazana ga rayuwa tare da lalata duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: