Hukumar kiyaye afkuwar cutuka masu yaduwa a Najeriya NCDC ta ce zazzabin Lassa ta hallaka mutane 142 a Najeriya.

Hukumar ta ce mutanen sun kamu da cutar ne a jihohi 23 na Najeriya.

Daga cikin jihohin da aka samu masu cutar akwai Bauchi, Ebonyi, Taraba, Rivers, Plateau, Nassarawa, Edo, da jihar Ondo.

Hukumar ta ce aan samu raguwar msu mutuwa a sanadin cutar la’akari da makonni 11 farkon shekarar 2022.

Daga jihohi 23 da cutar ta shiga ta tsallaka zuwa ƙananan hukumomi 97 daga cikinsu.

Sannan ta ce mafi yawa daga cikin waɗanda cutar ta kama su ne mutanen da ke tsakanin shekaru 21 zuwa 30.

Kuma aan fi samu mafi yawan masu cutar a jihohin Bauchi, Edo da jihar Ondo.

Leave a Reply

%d bloggers like this: