Kwararren mai haɗa bama-bamai ga mayaakan Boko Haram Awana Gaidam ya mutu.

Awanaa Gaidam ya mutu yayin da yake tsaka da haɗa wani bam da nufin kai wa jami’an sojin Najeriya hari a jihar Borno.
Gaidam wanda ke da sansaninsa a dajin Sambisa ya hada bama-bamai da aka yi amfani da su wajen kai wa jami’an tsaron Najeriya hari.

Masani kuma mai sharhi a sha’anin tsaro Zagazola Makama ya tabbatar da kutuwarsa.

Ya ce mutumin ya mutu a ranar Litinin.
Mutuwar Gaidam zai taba masu iƙirarin jihadi da aka fi sani da Boko Haram a cewar Zagazola.