Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da sabon shugaban hukumar kula da aikin yan sandan kasar.

An rantsar da Solomon Arase wamda tsohon sufeton yan sanda na kasa ne yau Laraba.
Sabon shugaban ya karbi rantsuwar fara aiki gabanin fara taron majalisar zartarwa da aka saba gudanarwa mako-mako.

Tuni majalisar dattawan Najeriya ta amince da shi bayan tantanceshi.

Kafin fara aikin, tsohon sufeton ya kammala aikinsa a shekarar 2016.
Sannan ya gaji tsohon shugaban hukumar kula da aikin yan sanda Maigari Dingyadi.