Zaɓaɓɓen gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya naɗa ƙwararren ɗan jarida Sanusi Bature Matsayin babban sakataren yaɗa labaransa.

Hakan na kunshe a wata sanarwa da shugaban kwamiti kan sha’anin mulki ya sanyawa hannu a madadin zaɓaɓɓen gwamnan.

Kafin naɗin, Sanusi Bature shi ne kakakin zaɓaɓɓen gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.

Sannna ya yi aiki da kafofin yada labarai na gida da na kasashen ketare.

Sannan ya taba tsayawa takara a shekarar 2019.

Injiya Abba Kabir Yusuf ya bayyan a Sanusi Bature a matsaayin jajirtacce mai riƙon amana wanda ya dace da kujerar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: