Jam’iyyar APC a jihar Kano ta shigar da kara a gaban kotun sauraaron korafe-korafen zaɓe a jihar.

Mai magana da yaawun jam’iyyar Ahmed Aruwa ne ya sanar da haka ya ce jam”iyyar ta shigar ta na mai ƙalubalantar zaɓen gwamna da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.
Jam”iyyar ta shigar da korafinta a kan hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC reshen jihar Kano daa kuma jam’iyyar NNPP.

Jam’iyyar tun a baya ta yi watsi da sakamakon zaɓen da INEC ta sanaar wanda ta ayyana Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano.

Ta ce sanar da zaɓen taa saɓa da dokar zaɓe ganin yaadda ta ce an tafka kurakurai a cikin sa.
Tuni hukumar ta shigar da korafin a gaban kotun wanda su ka bai wa masaana shari’a na jam’iyyar umarnin shigewa a gaba a shari’ar.
Tun a baya dan takarar gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya taya Abba Kabir Yusuf murna bayan da hukumar zabe INEC ta baa shi shaidar lashe zabe.