Hukumar NBC mai kula da kafofin yada labarai a Najeriya ta ci tarar miliyan biyar ga gidan talabijin na Chennel bayan sabawa dokar aikin jarida.

Kamar yadda shugaban hukumar ta NBC Balarabe Illelah ya bayyana a wata wasika da ya aikewa manema labarai.

Ya ce gidan talabijin na Chennel ya sabawa dokokin yada labarai shi yasa aka ci tararsa har kimanin naira miliyan biyar.

Balarabe ya ce a wata hira da gidan talabijin na chennel yayi da mataimakinn dan takarar shugabancin kasa na jamiyar Labour Party a ranar 22 maris Datti Baba ya ce ya sabawa dokar Najeriya a rantsar da shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu.

Don haka wannan kalamai za su jawo tinziri ga kasa a irin lokacin da ake ciki na barazanar tsaro.

Ya ci gaba da cewa gidan talabijiin na Chennel an dade ana ja musu kunne kan su san irin tattaunawar da za su yi da mutane don kaucewa barazana.

Balarabe ya ce an ci Talabijin tarar ne domin kaucewa irin wadannan abubwa a nan gaba don ta na sabawa dokokin yada labarai.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: