Rundunar yan sanda Najeriya hadi da jami’an tsaron farin kaya na DSS reshen jihar Legas sun ce sun yi nasarar kama jagoran yan awaren IPOB a jihar.

Kamar yadda kafafen yada labarai suka rawaito an bayyana yadda jami’an su ka kama wani shugaban yan aware na IPOB mai suna Nwajagu.
Nwajawagu shi ne wanda yayi alkawarin gayyatar yan kungiyar IPOB zuwa jihar ta legas ya ce domin bai wa yan kabilar Igbo mazauna jihar kariya.

kamar yadda aka rawaito ya bayyana ya ce ana kaiwa yan kabilar Igbo hari don haka ya gayyacci yan aware da su shiga yankin domin bada kariya.

Sai dai jamian yan sanda da DSS sun kama wanda ake zargin a cikin wani otel bayan ya bar gida.