Jam’iyyar APC a Najeriya ta bayyana dalilai da ya sa su ka rasa kujerar gwamna a Kano yayin da aka ayyana jamiyyar NNPP a maatsayin wadda ta lashe zabe.

Shugaban jamiyyar na ƙasa Sanata Abdullahi Adamu ya ce son zuciya na daga cikin dalilai da ya sa su ka rasa kujerar gwamna a Kano.

Shugaban ya zargi wasu ƴan jam’iyyar da yin kafar ungulu hayan su a matakin tarayya sun yi duk abinda ya kamata.

Ya ce duk abinda za a yi Kano ake sakawa a gaba a don haka ba su taɓa tsammanin za su rasa kujerar gwamna ba.

Duk da cewar shugaban bai fito fili ƙarara ya bayyana mutanen da su ke zargi da son zuciya ba, sai dai ya ce sun ja hankalin dukkan gwamnonin jamiyyar APC a kan su guji sin zuciya gudun kada su batawa mutane rai.

Sannan ya ce jamiyyar za ta ɗauki mataki a kna duk wanda ya yi musu abinda bai kamata ba.

Ya ce ya na da yakini za su lashe zaɓe da za a kammala a jihohin Kebbi da Adamawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: