Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce jami’anta sun dakile wani mummunan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Tsafe ta jihar.

Kakakin rundunar, Mohammed Shehu, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi 9 ga watan Afrilu, ya ce an kuma hallaka wasu ‘yan bindiga biyu yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Shehu ya ce Kolo Yusuf, kwamishinan ‘yan sandan jihar ya yabawa jami’an rundunar bisa namijin kokarin da suka yi, ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su hada kai da jami’an tsaro a kokarin tabbatar da tsaro a jihar.

A bangare guda, kwamishinan ya yiwa mazauna jihar alkawarin tabbatar da kokari da ci gaba da yakar ‘yan ta’addan da suka addabi jihar da ke Arewa maso Yamma.

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fuskantar matsalolin hare-haren ‘yan bindiga da masu sace mutane da neman kudin fansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: