Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Adamawa Ahmad Fintiri ya karɓi shaidar lashe zaɓe a yau Laraba.

Fintiri ya lashe zaɓen gwamna a karo na biyu da ƙuri’u sama da dubu ɗari huɗu.

Sai dai an samu ruɗani a zaɓen yayin da tsohon shugaban hukumar zaɓe na jihar ya ayyana Aisha Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamna a jihar.

Daga bisani hukumar zaɓen a Najeriya INEC ta dakatar da faɗar sakamakon tare da dakatar da shugaban hukumar.

An ci gaba da karɓar saamakon zaɓen gwamnan a jiya Talata kuma ahukumar ta tabbatar da sanarar Ahmad Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna a jihar.

An bai wa Ahmad Fintiri shaiar lashe zaɓen gwamnan jihar a shalkwatar hukumar INEC da ke babban birnin tarayya Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: