Firaministan United Kingdom (UK), Rishi Sunak, ya rubuto wata takarda ta musamman zuwa ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, kafin zuwan ranar rantsar da shi kan karagar mulki.

A wata wasiƙa da jaridar The Cable ta ruwaito Sunak ya bayyana cewa a shirye ya ke ya yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Tinubu, wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC, a watan Fabrairu.
Sunak ya bayyana cewa yana fatan ya tarbi Tinubu a birnin Landan a watan Afirilun 2024, a wajen taron zuba jari a nahiyar Afirika kashi na biyu.

Taron zai kasance wani lokaci mai muhimmanci domin ƙara ƙarfafa dangantakar kasuwancin Najeriya da UK, domin samar da ayyukan yi da cigaba, ƙara zuba jari a ƙasashen biyu da kasuwanci da kuma taimaka masa wajen ɓunƙasa ƙarfin fitar da kaya zuwa ƙasashen waje.

Ya ce za su iya ƙara ƙarfafa dangantakar su, ta hanyar ƙarfafa alaƙar kasuwanci da zuba jarin su, domin amfanin ƙasashen su gabaɗaya, ta hanyar ƙara ƙarfin danƙon kasuwanci da zuba jari.
The Cable tace firaministan ya ce UK za ta cigaba da taimaka wa Najeriya wajen magance matsalar tsaro, ta hanyar ba ta horarwa da kayan aiki.