Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya amince da nadin Muhammad Aliyu a matsayin sabon babban sakatare a hukumar jin dadin Alhazai ta jihar.

A cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Neja ya fitar a safiyar yau Alhamis a birnin Minna, sanarwar ta bayyana cewa nadin Muhammad Aliyu akan wannan mukami yazo ne bisa cancanta, kwarewa, gaskiya, kwazo da kuma kwarewar aiki na tsawon lokaci.
Ana sa ran sabon sakataren zai yi aiki bisa bin tsarin aiki da manufofin hukumar jindadin alhazai ta jihar.

Gwamna Abubakar Sani Bello ya taya sabon babban sakataren murna tare da bukatarshi da yayi aiki bisa gaskiya da amana.

Kamfanin dillancin labarai na kasar NAN ya bayar da rahoton cewa Aliyu zai maye gurbin Maku Lapai a matsayin sabon babban sakataren hukumar.