Kwamitin lura da tattalin arziki na kasar nan na duba yiwuwar kara wa’adi daga watan Yuni na wannan shekarar akan batun janye tallafin akan man fetur.

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmad Shamsuna ce ta haska hakan a yau Alhamis, bayan kammala zaman kwamitin da mataimaki shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar Shugaban kasa Villa da ke Abuja.
Ta kuma ce dukkan wasu shirye-shirye za’a cigaba da tuntuba ga jihohi da masu ruwa da tsaki, ciki har da wakilan daga gwamnati mai zuwa.

Ta bayyana cewa majalissar ta aminta da cire tallafin farko tun da wuri saboda ba mai dorewa bane, ya kamata a yishi ta yadda hakan zai amfani kowanne dan Najeriya.

Ta kara cewa in zata tunatar kasafin kudin shekarar 2023 ya samar da tallafin ne iyakar watan Yuni, sannan dokar man fetur ta samar da bukatuwar duk abubuwan da suka shafi man fetur dole a sauya dokarsu watanni 18 bayan ainahin lokacin cirewar. Wanda wannan lokacin zai kai har watan Yuni na wannan shekarar.