Ƴan ta’addan ƙungiyar ISWAP, sun sace jami’an tsaro biyu da masu aikin jin kai guda uku a jihar Borno.

Masu aikin jinkan ma’aikatan ƙungiyar bayar da jinƙai ce ta Family Health International, FHI 360.
Ƙungiya ce mai zaman kanta (NGO) ta ƙasar Amurka.
Channels Tv ta ruwaito cewa ma’aikatan guda uku waɗanda duk maza ne, an neme su an rasa ne a gidan da suke zaune a Ngala, wani gari da ke a tsakanin iyaka da tafkin Chadi.

Duk da dai ana zargin cewa ƴan ta’adda ne suka sace su, jami’an tsaron sojoji da ƴan sanda, har yanzu ba su ce komai ba dangane da lamarin.
Amma wata majiya ta bayyana cewa wasu jami’an tsaro guda biyu na kamfanin tsaro na Halogen, waɗanda su ke aiki tare da FHI 360, su ma an neme su a rasa a lokaci ɗaya da aka yi awon gaba da ma’aikatan jinƙan.

Majiyar wanda ma’aikacin lafiya ne mai aiki da FHI 360 a Ngala, ya bayyana ya ce Ma’aikatan su ne, sun tashi ranar Laraba ba su gan su ba, tare su ke rayuwa da su a gidan, amma ba su ji ƙara ko wani sauti da zai sanya su fahimci wani abu na aukuwa ba.