Majalisar tattalin arziki ta gwamnatin Najeriya (NEC) ta dakatar da shirin zare tallafin Man Fetur a karshen gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Ministar kuɗi, kasafi da tsare-tsaren ƙasa, Zainab Ahmed, ce ta bayyana haka yayin zantawa da ‘yan jaridan gidan gwamnati jim kaɗan bayan kammala taron NEC.

Rahoton Vanguard ya ce taron NWC ɗin ya gudana karkashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a Aso Villa, birnin tarayya Abuja.

Zainab Ahmed ta ƙara da bayanin cewa shirin cire tallafin Man Fetur ɗin zai fara aiki ne daga watan Yuni, 2023 saboda kasafin kuɗin 2023 ya ware tallafin har zuwa watan Yuni.

A cewarsa duk wani jinkiri na cire tallafin da aka samu zai bukaci garambawul a kundin dokokin man Fetur (PIA) da kuma kasafin kuɗin wannan shekarar da muke ciki.

Ministan ta ce babu wani sabon wa’adin cire tallafin da NEC ta sanya, a halin yanzun sun bar wuƙa da nama hannun gwamnati mai zuwa, ita zata yanke cirewa ko akasin haka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: