Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna a Najeriya (NAFDAC) ta gargadi ‘yan Najeriya game da wani magani mai kisa da ke yawo a kasar, NATURCOLD.

Babbar Daraktar NAFDAC, Mojisola Adeyeye ce ta bayyana gargadin a ranar Laraba, 26 ga watan Afrilun 2023, kuma ta ce rahotanni sun ce maganin ya kashe yara shida a kasar Kamaru.

Daraktar ta NAFDAC ta ce, maganin na tari ne, kuma babu shi a jerin magungunan da ta amince dasu wadanda aka shigo dasu daga kasashen waje.

Daga nan, ta ce ya kamata a kula da shigowa da kuma yawon magunguna marasa inganci, lasisi da tasiri a kasar nan, masu siya suke dubawa da kyau.

Ta kuma bukaci masu shigo da magunguna, dillalai da masu saye da su guji shigowa da amfani da bogin magani a kasar.

Ta yi karin haske da cewa, magungunan bogi suna shiga Najeriya ne ta kasashen makwabta, kuma ana siyar dasu ne a kasuwar bayan fage a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: