Wata babbar Kotu a Jihar Ekiti ta yankewa wani mai suna Isma’il Ojo hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon samunsa da laifin hallaka wani makwabcinsa mai suna Kareem Audu akan babur.

Kotun ta yankewa Ojo hukuncin ne bayan da dan sanda mai shigar da kara ya shaidawa kotun cewa matar wanda aka hallaka ta shigar da karafi a ofishinsu cewa wani mai suna Isma’il Ojo ya hallaka mijinta sakamakon takaddama akan mallakar wani babur.


Alkalin kotun Justis Olasegun Ogunyemi ya bayyana cewa bayan gabatarwa da kotun hujjoji da shaidu kotun ta tabbatar da wanda ake zargin ya aikata kisan ta hanyar shake wuyan Kareem.
Olasegun ya bayyana cewa an yanke masa hukuncin ta hanyar rataya.
Wanda aka yankewa hukuncin ya bayyana cewa yana wanka wanda ya hallaka yazo ya daukar masa babur bayan ya ajiye shi a kofar gida.
Yace bayan ya gama wankan ya je gidan Kareem Audu a lokacin yana bacci ya kasheshi, inda yace yaje ne badaniyyar hallaka shi ba.
An gurfanar da wanda ake zargin ne a gaban kotun tun a ranar 13 ga watan Mayun shekarar 2018 da ta gabata.