Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Ya nada sababbin Hakimai guda shida.

Da yake jawabi lokacin da aka nada Hakiman, Mai Martaba Sakin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace an nadasu Sarautun ne bisa cancantarsu da irin gudunmawar da suke bayarwa a cikin al’umma.
Wadanda aka nada Sarautun sun hadar da Alhaji Abbas Maje Ado Bayero a Matsayin Bauran Kano da Alhaji Kabiru Ado Bayero a Matsayin San Turakin Kano da Alhaji Umar Ado Bayero wanda aka nada shi Yariman Kano.

Sauran sune Alhaji Tijjani Ado Bayero a Matsayin Zannan Kano da Alhaji Auwalu Ado Bayero a Matsayin Sadaukin Kano da Alhaji Ado Ado Bayero a Matsayin Cigarin Kano.

Mai martaba Sarkin Kano ya horesu dasu Sanya halayyar magabatansu na yin koyi da kyawawan halaye wadanda suka hadar da Juriya da hakuri da amana da tausayawa talakawa.
Yace su dauki halayyar magabata ta mika dukkan al’amuransu ga Allah tare da yin biyayya ga wadanda suka tarar a cikin tsarin hakimci da kuma yin da’a kamar yadda suka taso su ka ga ana yi Kasancewarsu dukkanninsu yan gidan sarautar Kano ne.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci hakiman da aka nada su zamo jakadu nagari a duk inda suka samu kansu tare da gudanar da aikinsu da gaskiya da amana tare da Sanya tsoron Allah.