Alummar garin Wanzamai da aka yi garkuwa da yaransu akalla 95 zuwa 100 sun saiyar da gidajensu da gonakin su wasu kuma bara su ka yi kafin sakin yaransu da aka yi garkuwa da su a kwanakin baya.

Idan ba a manta ba sama da makonni uku da suka gabata ne wasu da ake zargin yan bindiga ne suka shiga garin Wanzamai tare sace akalla mutane 95 a yayin da suke yin aikin gona a karamar hukumar tsafe ta jihar Zamfara.
Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa Allah ne ya karbi adduoin su da suke yi tun da lamarin ya faru a wanzamai.

Ya ci gaba da cewa wadanda aka yi garkuwan da su dukkaninsu maza da matan sun rame kamar basa cin abinci kuma yanzu haka suna asibiti ana duba lafiyarsu.

Sannan wani daga cikin shaidan ya ce sai da suka biya kudade ta hanyar sai da gonakinsu gidajensu tare da neman taimako kafin kaiwa yan bindiga su saki wadanda aka kama.
Sai dai ya ce yanzu haka yan garkuwar sun saki 75 daga cikin wadanda suka hada maza da mata yan kasa da shekaru 20 sai kuma dattijai Hudu kuma sun hallaka matasa biyu.
Sannan suna rike da mutanen 25 wadanda busu sake su ba.
Kamar yadda yake ikirari shugaban kasa Muhammadu Buhari yana mai cewa yayi nasara a lamarin tsaron kasar a mukinsa na shekaru Takwas.