Hukumar dake dakile masu yiwa tattain arzikin kasa ta’anati EFCC ta bukaci tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom Godwills Akpabio ya bayyana gabanta domin amsa tambayoyi.

Akpabio wanda dan majalissa ne daga jihar Akwai Ibom ya bayyana a gabanta daya daga cikin masu neman kakakin majalissar.

Hukumar ta EFCC ta ce ta na mai neman sanata Akpabio domin tuhuma da ta ke masa.

Sai dai tun a watan Maris din da ya gabata hukumar ta nemi da ya hallara a gabanta inda ta mikawa lauyansa Umeh takardar neman.

Sai dai lauyan ya bayyana cewa Sanata ba zai samu damar zuwa ba saboda yana da ganin likita a ranar 29 ga watan.

Ya ce Akpabio yana fama da cutar limoniya da kuma sauran cututtuka ibin da take ga har taba masa zuciya, don haka ba zai samu damar amsa gayyatar ba har sai bayan azumi.

Hukumar ta EFCC ta kara mika goron gayyatar ga dan majalissar saboda tana da wasu tuhume tuhume da ta ke yi masa kuma ya bada amsa.

tun a shekarar 2015 EFCC ta zargi Godwills Akpabio bisa tuhumarsa da wasu makudaden kudade har kimanin Biliyan 108 lokacin da yana gwamnan Akwai Ibom.

Leave a Reply

%d bloggers like this: