Gwamnatin tarayyar Najeriya ta haramtaa shigar da taliyar Indomie cikin ƙasar.

Hakan ya fito daga bakin shugabaar hukukar kula da ingancin abinci da magunguna aa Najeriya Mojisola Adeyeye ta yi a yau Litinin.

Ta ce an ɗauki matakin hakan ne bayan da hukumomin wasu ƙasashe su ka yi zargin akwai sinadarin da ke haddasa ciwon daji wato kansa a cikin taliyar.

Sannan ɓangare kula da sinadarai a hukumar sun dukufa domin zurfafa bincike a kan sinadarin da ake zargi ya na haifar da ciwon daji a cikin taliyar.

Shugabar ta ce tun tuni gwamnatin da hukumar Nafdac a Najeriya ba su bai wa kamfanin Indomie lasisin shigar da kaya ba.

Haka kuma an shafe tsawon shekaru da haramta shigar da ita cikin Najeriya.

Ta ce sanarwar hakan sun yi ne domin sake jan kunnen mutane da masu shigar da ita a kan dokar domin ba sabuwar doka ba ce.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: