Kungiyar kwatago a Najeriya ta ce ma’aikata a ƙasar sun shiga wani yanayi tun bayan da shugaba Buhari ya karɓi ragamar mulkin ƙasar.

Ƙungiyar ta ce babu wani sauyi na cigaba da su ka smau tun da shugaba Buhari ya karɓi ragamar mulkin ƙasar.
Sakataren kungiyar a Najeriya Kwamared Nasir Kabir shi ne ya bayyana haka yayin tattaunawarsu da BBC.

Ya ce suj yi faarin ciki da zagayowar ranar ma’aikata ta duniya wadda majalisar ɗinkin duniya ta ware domin su.

Sai dai su na takaici a bisa halin da ma’aikata ke ciki a Najeriya.
Ya bayyana cewa tashin farashin kayyayaki a ƙasar sun haifar da koma baya musamman batun tsadar man fetur, tsadar wutar lantarki, da tsadar kayan masarufi.
Sannan ya koka a kan karancin albashi daa ma’aikata ke fuskanta a kasar, wanda ya bayyana hakan a matsayin barazana.
Ya ce ma’aikata bbau abinda su ka samu a mulkin shugaba Buhari banda koma baya.