Hukumar Kula da Aikin jindadin Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta ba wa Kamfanin Max Air aikin jigilar maniyyatan Jihar Kano su 5,917 zuwa Saudiyya domin sauke farali a Hajjin bana.

Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Muhammad Abba Dambatta ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Talata.
Idan za’a iya tunawa a baya an ruwaito cewa matakin da NAHCON ta dauka na ba wa Kamfanin Azman Air jigilar maniyyatan jihar a shekarar da ta gabata ya fuskanci gagarumar suka daga Hukumar Jin dadin alhazai ta Jihar Kano da kuma gwamnatin jihar.

Kamfanin Max Air dai ya dade yana jigilar alhazan jihar har zuwa shekarar da ta gabata a lokacin da sabon Shugaban Hukumar NAHCON ya ba wa Kamfanin Azman Air aikin jigilar.

Ya kara da cewa jirgin yana da inganci kuma yana da jiragen sama guda uku masu daukar fasinja 1,000 , wanda hakan zai kawo saurin kwashe maniyyatan a bana.
Haka kuma, Muhammad Dambatta ya sanar da cewa hukumar ta rufe yin sabuwar rajistar aikin Hajjin sakamakon umarnin da NAHCON ta bayar.
A cewarsa, an samu kujeru kusan 6,000 da Hukumar NAHCON ta ware wa maniyyata a jihar Kano.