Hukumar kula da aikin dan sanda a Najeriya PSC ta amince da biyan albashin sabbin jami’anta.

Hukumar ta amince da biyan sabbin jami’an bayan shafe watanni shida su na aiki.

Sabbin maaikatan da su ka fara aiki bayan samun horo a makarantar horas da aikin dan sanda.

Shugaban hukumar Dr. Solomon Arase ne ya shaida hakan wanda ya bukaci sauran jami’an da su tabbata sun cika sharudan samun albashi a gwamnati ta gindaya.

Sanarwar wadda mai maganaa da yawun hukumar Ikechukwu Ani ya sanya hannu ranar Lahadi, ya ce hukumar ta amince da fara biyan albashin sabbin yan sanda 1,007.

Hukumar ta ce ta dukufa domin ganin aikin ya kammala tare da tabbatar da fara biyan sabbin jami’an.

Leave a Reply

%d bloggers like this: