Majalisar jihar Sokoto ta yi wata sabuwar doka ta rage yawan kuɗaɗen da ake kashewa a wajen bukukuwan aure a jihar.

Ɗan majalisa da ke wakiltar ƙaramar hukumar Yabo, Alhaji Abubakar Shehu na jam’iyyar APC da kuma takwaransa da ke wakiltar ƙaramar hukumar Gudu, Faruk Balle na PDP sune suka gabatar da ƙudurin a gaban majalisar a jiya Talata.

Abubakar Shehu wanda ya kasance shine shugaban kwamitin Addini na majalisar, ya gabatar da ƙudurin wanda kuma ya samu karɓuwa da kaso mafi rinjaye na majalisar.

A kudurin an buƙaci a rage yawan almubazzaranci da kuɗaɗen da ake yi a yayin bukukuwan aure, suna, shayi da kuma wasu sauran bukukuwa na al’ada da akan gudanar a jihar.

A yayin da ya ke gabatar da ƙudurin, Shehu ya ce kwamitin nasu ya yi zama da masu ruwa da tsaki, waɗanda suka bada ƙarin wasu shawarwarin da suke a ƙunshe cikin ƙudurin.

Bayan tattaunawa tsakanin ‘yan majalisun a zaman da mataimakin kakakin majalissar ta Sokoto Alhaji Abubakar Magaji ya jagoranta, ‘yan majalissun sun amince da tabbatar da ƙudurin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: