Hukumar jami’ar jihar Filato (PLASU) da ke arewa ta tsakiya a Najeriya ta tabbatar da cewa wasu miyagun ‘yan bindiga sun kai hari ɗakunan kwanan ɗalibai mata.

Ta ce ‘yan bindigan sun kai harin a tsakanin daren ranar Talata, 9 ga watan Mayu zuwa wayewar Laraba da nufin garkuwa da ɗalibai mata.

Hukumar jami’ar ta bayyana cewa jami’an tsaron makarantar sun samu nasarar daƙile yunkurin ‘yan bindigan na shiga dakin dalibai mata tun kafin su ɗauki kowa.

Jami’in hulɗa da jama’a na jami’ar jihar Filato, Mista John Agams, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar.

Agams ya ce ‘yan ta’addan sun kai farmaki makarantar ne da nufin sace ɗalibai amma suka kwashi kashinsu a hannun jami’an tsaro, waɗanda suka daƙile harin.

Kanfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya ce har kawo yanzu hukumar yan sanda reshen jihar Filato ba ta ce komai ba game da harin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: