Hukumar ƙididdiga a Najeriya ta ce an samu ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a watan Afrilun da ya gabata.

Hukumar ta ce ƙaruwar ya hauhawa da kaso 22.22 kamar yadda rahoton da su ka fitar ya nuna.
A watan Maris na shekarar da mu ke ciki an samu hauhawar farashin da kaso 22.04 wanda aka samu hauhawar farashi a watan Afrilu da 0.18.

Daga cikin kayayyakin da farashin su ya hauhawa akwai kayan abinci, farashin Gas,fetur da sauran kayan amfani.

Haka kuma an samu hauhawar farshin surufi musamman na matafiya a titi da kuma matafiya a sararin samaniya.
Sannan frashin magunguna ma na daga cikin abubuwan da su ka tashi a watan.
Farashin kayayyaki na ci gaba da hauhawa la’akari da shekarar da ta gabata ta 2022.