Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce ta fara shirin domin ganin an samar da isashen tsaro a ranar rantsar da sabbin shugabannin da aka zaɓa a kasar.

Sufeton yan sanda na ƙasa Usman Alƙali Baba ne ya bayyana haka wanda ya ce za su tabbatar an yi hakan ba tare da an samu wata matsala ba.
Sannan ya yi alkawarin kare martabar demokraɗiyyar ƙasar, tare da ganin an gudanar d komai cikin tsari da zaman lafiya.

Si dai sufeton ya gargaɗi ƴan siyasar Najeriya da su ke yunƙurin tayar da fitina a rnar da su kiyaye tare da ƙauracewa haka.

Ya ce ba z su zuba idanu har a samu wta matsala yayin rantsar da sabbin shugabannin ba.
Sannan ya hori ƴan ƙasar da su kasance masu mutunta martabar demokaraɗiyya tare da kare mutuncinta a idon duniya.