Hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta kasa Najeriya FRSC ta bayyana cewa cikin shekara guda fiye da  mutane 40,000 ke rayuwarsu a Najeriya.

Shugaban hukumar Dauda Biu ne ya bayyana haka a wani taro da ya gudana a ABUJA.

Taron wanda aka yi karo na Bakwai kamar yadda majalisar ɗinkin duniya ta tsara don a kan kiyaye afkuwar haddura.

Ya ce mutane miliyan 1.3 ke mutuwa a duniya yayin da fiye da mutane miliyan 50 ke smaun rauni sanadin haddura a duniya.

Shugaban ya ce majalisar ɗinkin duniya ta samar da wani tsari da za a aiwatar a duniya domin takaita afkuwar haddura.

Makon taron da za a yi, hukumar ta haɗa kai da hukumar lafiya ta duniya, da ma’aikatar lafiya ta Najeriya da wasu hukumomi domin shirya tare da aiwatar da ayyukan makon karo na bakwai a shekarar 2023.

Taken makon na bana shi ne #Rethinkmobility wato sake tunani domin samar da ci gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: