Zababben shugaban kasar Najeriya mai jiran gado wato Bola Ahmad Tunubu yayi wata ganawar sirri da Da Rabiu musa Kwankwaso a birnin Paris.

Kamar yadda sanarwa ta bayanna ta ce an yi ganawar ne cikin sirri a kasar Faransa.

Ganawar da aka yi da tsohon gwaman jihar kano kuma dan Takarar shugaban kasa a jamiyyar NNPP a zaben da ya gabata ya samu nasarar zuwa na hudu bayan tunubu ya lashe zabe.

Sannan tattanawar da ba wanda ya san takamaimai akan abun da aka yi.

sai dai ana ganin ba za ta wuce nasaba da yadda za a tsara gwamnati ba a Najeriya.

Zababben shugaban kasa Bola Tunubu har yanzu bai bayyana yadda zai gudanar da mulkinsa ba yayin da saura kwanaki kalian a yi rantsuwa 29 ga Mayu.

Sai dai wasu na ganin ko dai tafiyar za ta iya kasancewa an sanya kwankwaso a tsarin tafi da gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: