Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, a birnin tarayya Abuja, ta sake ɗage zaman fara sauraron ƙarar da Peter Obi ya shigar kan nasarar Bola Tinubu.

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa, kotun ta ɗage sauraron ƙarar ne har zuwa ranar Juma’a, 19 ga watan Mayun 2023.
Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP), yana

ƙalubalantar nasarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya samu a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Peter Obi ya halarci cigaba da zaman fara sauraron ƙarar na yau Laraba, 17 ga watan Mayun 2023.
Sai dai Kotun wacce mai shari’a Haruna Tsammani ya ke jagoranta, ta ɗage sauraron ƙarar ne, saboda ɓangarorin biyu sun kasa cimma matsaya akan wasu takardu da kuma wasu hujjoji.