Uwargidan shugaban ƙasa, Hajiya Aisha Buhari ta ce za a riƙa tuna mijinta Shugaba Buhari a matsayin shugaban ƙasan da ya bai wa matasa muhimmanci.

Ta bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da wani shirin tallafin lafiya ga mutanen karkara (HIRD), na hukumar matasa masu yi wa ƙasa hidima, NYSC, a Abuja.
Ta ƙara da cewa shugaba Buhari mutum ne da ke matuƙar son shirin na masu yi wa ƙasa hidima wato NYSC, saboda yadda ya ke son ganin haɗin kan ‘yan Najeriya.

Ta ƙara da cewar saboda ƙaunarsu da Buhari ya ke yi, sukan gayyaci matasan masu yi wa ƙasa hidima zuwa gidansu da ke Daura a duk lokacin bukukuwan Sallah.

Aisha Buhari ta yi kira ga masu gudanar da shirin da kada su yi ƙasa a gwuiwa wajen tabbatuwar haɗin kan ‘yan ƙasa ta hanyar
A nasa bangaren, babban Darakta na hukumar masu yi wa ƙasa hidima, NYSC, Birgediya Janar Yushau Dogara Ahmed ya ce an ƙirƙiro shirin na HIRD ne a shekarar 2014 saboda taimakawa marasa ƙarfi da ke a yankunan karkara.
Ya ce shirin ya ƙunshi ‘yan bautar ƙasa da suka haɗa da likitoci, masu bada magunguna, ma’aikatan jinya, likitocin haƙori da sauransu, waɗanda suke duba marasa lafiya a kyauta.