Mai bai wa shugaban ƙasar Najeriya sha’awara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Mongonu ya bai’wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa za a samar da wadataccen tsaro a yayin rantsar da sabuwar gwamnatin Najeriya wanda za a gudanar a ranar 29 ga watan Mayu.

Janar Mongonu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a burning tarayya Abuja wajen wani taro da aka gudanar kan shirye-shiryen bikin ranar rantsuwa.
Mongonu Wanda ke jagorantar kwamitin tsaro a shirye-shiryen Mika mulki ga sabuwar gwamnati ya bayyana cewa sun Samar da tsauraren matakai domin tabbatar do tsaro a lokacin bikin rantsuwar.

Babagana ya bayyana cewa za su Samar da isasshen tsaro a Eagle Square inda za a gudanar da rantsuwar da Kumar guraren da ke kusa.

Janar Monguno mai ritaya ya ce an tanadar wa da masu ababan hawa hanyar da za su domin za a takaita zirga zirga a gurin da za a gudanar da rantsuwar.
Sannan yayi kira ga ‘yan Najeriya da su gujewa tayar da zaune tsaye a lokacin tare da bayar da tabbacin gudanar da taron cikin koshin lafiya.