Majalisar Tarayyar Najeriya ta amince wa shugaban Kasa Muhammad Buhari da ya karbo bashin dala miliyan 800.

Mamba a kwamitin kula da karbo bashi a majalisar wakilai Hon Abubakar Yunusa Ahmad ne ya bayyana hakan.

Hon Abubakar ya tabbatar da hakan ne ta cikin shirin Sunrise Daily na gidan Talabijin na Channels a ranar Juma’a.

Yunusa ya bayyana cewa kafin amincewar majalisar sai da aka kafa sharuddan cewa ba za su bar gwamnatin ta shugaba Buhari mai barin Gado ta kashe dukkan kudaden da ta karbo bashi ba.

Abubakar ya kara da cewa sabuwar gwamnati mai jiran gado ta na da hakkin kawo nata tsarin wanda zai amfanar da ‘yan Najeriya.

Ahmad ya ce itama sabuwar gwamnati mai zuwa ta na da nata abubuwan da za ta tunkara da kudaden ba kamar gwamnati mai barin gado ba

Leave a Reply

%d bloggers like this: