Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da babbar matatar man fetur mallakin attajiri Alhaji Aliko Dangote.

An ƙaddamar da babbar matatar a jihar Legas bayan shafe shekaru ana ginawa.

Mammalakin matatar Aliko Dangote y ace shugaba Muhammadu Buhari na daga cikin mutanen da su ka ƙarfafeshi wajen kammala aiki.

Ya ce a baya ya so jingine aikin sai dai ya samu ƙarfin gwiwa daga shugaba Buhari wanda ya ƙarfafeshi yayin da ya karaya.

Matatar na da manyan tankuna 177 wanda za su iya ɗaukar mai da ya kai yawan lita biliyan 4.742.

An gina ta a Ibeju-Lekki a jihar Legas kuma ake sa ran za ta dinga tace danyen mai da ya kai ganga 650,000.

Kasancewar irinta ce mafi girma a faɗin duniya, an tsara yadda za ta dinga sarrafa danyen mai daga kasashe daban daban na duniya.

A na sa ran za ta wadatar da Najeriya da man da ta ke buƙata har ma a dinga fitar da wani zuwa maƙoftan ƙasashe.

Biƙin buɗe babbar matatar ya samu halartar wasu daga shugabannin ƙasashe da kum manya daga shugabannin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: