Babban bankin Najeriya (CBN) ya kara kudin ruwa zuwa kashi 18.5 cikin dari don dakile hauhawan farashin kayayyaki.

A makon da ya gabata, tashin farashin kayayyaki a kasar ya haura zuwa kashi 22.22 musamman farashin kayan abinci.

Gwamnan babban banki, Godwin Emefiele ne ya tabbatar da haka a yau Laraba 24 ga watan Mayu ga manema labarai a sakatariyar bankin da ke Abuja.

Wannan shi ne karo na uku da babban bankin ke kara kudin haraji a wannan shekara.

Idan ba ku mantaba a baya ma bankin ya kara farashin kudin kamar yadda manema labarai suka ruwaito

Leave a Reply

%d bloggers like this: