Babbar kotun dake sauraron shari’ar zababen dan majalissar tarayyar Doguwa da Tudun Wada Alhasan Ado ta wanke shi daga zargin da ake masa na tuhumarsa da kisan kai a yayin zabe.

Babban lauyan jihar kuma kwamishinan sharia Musa Abdllahi Lawan shi ne ya shadawa yan jarida a safiyar ayau Ahamis.
Ya ce bayan dogon nazari da kotun ta yi akan Alhasan Ado Doguwa kotu ta gano cewa shi ba mai laifi bane a lamarin.

Ana zargin Alasan Ado Doguwa da kisan mutane tare da kona su da wuta a lokacin da ake zaben da ya gabata.

Sai dai yanzu haka kotu bisa rashin shaidu kwarara ta wanke shi da tuhumar kisan kai da ake yi masa.
Kwamishinan ya ce kotu ta rasa laifin da za ta kama shi da shi na kisan kai da kona mutane don haka ta kori karar.