Jirgin farko na maniyyata aikin hajjin bana a Jihar Ogun sun sauka a babban filin tashi da sauka na Sarki Mahammad Abdulaziz dake kasar Saudiya.

A ranar Talata ne dai aka sanar da zuwansu kasar ta Saudiya da misalin karfe 8:36 na safe.
Sakataren hukumar Jin dadin Alhazai ta jihar Ogun Alhaji Sallau Dauda ne ya bayyana haka ga yan Jaridu.

Ya ce akalla maniyyata 439 ne suka sauka a kasar Saudiya wadanda za a su yi aikin hajjin.

Maniyyatan sun tashi a jirgin mai namba A330 a filin jirgi na Muratala Muhammad dake Ikeja birnin jihar Legas a ranar Litinin 10 :45.
Ya ci gaba da cewa jirgi na biyu sunan a shirye domin tafiya.
Sannan ya ce ana saran ranar Alhamis za a kammala dibban maniyyatan su 1,234 ne jihar Ogun.