Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa masu kananan sana’o’i ba za su na biyan haraji ba da za a fara karba a watan Yuni mai kamawa.

Gwamnan ya bayyana cewa masu kananan sana’o’i wadanda ba za su biya harajin ba sune wanda kudin shigan da suke samu ya gaza Naira 30,000.
Ya kara da cewa karbar haraji a wurin irin wadannan mutane rashin adalci ne saboda yanayin yadda rayuwa ta yi tsada.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan bai fadi wani tsari ta yadda gwamnatin za ta gane masu kananan sana’o’i da ake magana akansu ba.

Abba Kabir ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta samar da kyakkyawan yanayi da kuma samar da jari don kananan masana’antu a jihar don bunkasa tattalin arziki.
A cewar sa zasu dawo da bankunan ba da rance guda 37 da gwamnatin Kwankwaso ta kirkira don habaka harkan kasuwanci, wadannan bankuna su ne gwamnatin tsohon Ganduje ta bar su kara zube don samun damar siyar da su ga abokansu da ‘yan uwansu.