Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa INEC reshen Jihar
Kaduna ta tabbatar da aslin wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar.

Hukumar ta ce dan takarar gwamnan karkashin Jam’iyyar APC Sanata Uba Sani shine ya samu nasara a zaben da aka gudanar tun a ranar 18 ga watan Maris din shekarar da muke ciki.

INEC ta bayyana hakan ne a lokacin da ta ke ankarar da kotun karbar karar rakin zabe dangane da wani babban kuskure da ya saba wa kundin tsarin mulki Najeriya a cikin karar da jam’iyya PDP ta shigar inda ta ke kallubalantar nasarar da Jam’iyya mai mulki ta APC ta samu a Jihar.

Hukumar ta ce sabon gwamna mai ci a yanzu a Jihar Sanata Uba Sani ya samu masara ne ba tare da boye-boye ba kuma bisa tsarin doka aka aka sanar dashi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben.

Jam’iyyar ta PDP a Jihar ta shigar da kara gaban Kotun ne bayan ayyana Sanata Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar, inda ya kayar da abokin takarar na Jam’iyyar PDP Mohammed Ashiru Sani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: