Shugaban Kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin ba da tallafi ga ‘yan Najeriya domin rage musu radadin cire tallafin man Fetur da Gwamnatin yi.

Shugaban Kamfanin Mai na Kasa NNPCL Mele Kyari ne ya sanar da hakan yana mai cewa biyan tallafin mai da gwamnati ke yi ya zama tarihi sannan ba za a ware masa ko sisi ba idan an tashi kasafin kudi.
Male Kyari ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da jagororin jam’iyyar mai mulki ta APC inda ya ce a halin yanzu ma NNPC na bin gwamnati bashin Naira tiriliyan 2.8 da ya kashe wajen biyan tallafin man.

Kyari ya bayyana cewa babu wani wanda zai kara bayar da bashi ga wanda yake bi bashin Naira tiriliyyan 2.8,inda ya ce kamfanin NNPCL ba zai iya kara biyan tallafin Mai a madadin gwamnati ba.

Mele ya kara da cewa kudin da kamfanin mai na NNPC ke kashewa wajen biyan tallafin na hana shi sauke nauyin da ya rataya a kansa sannan Kasa na bukatar kudaden aiwatar da manyan ayyuka da samar da ababen more rayuwa.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matakan da za su hana cire tallafin man wanda hakan ka iya jefa ’yan kasar cikin karin matsin rayuwa.
A gefe guda kuma, kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dauki matakan da za su hana cire tallafin man jefa ’yan kasar cikin karin matsin rayuwa.
Mukaddashin daraktan Amnesty International Isa Sanusi ya shawarci gwamnati ta yi hattara kada matakin nata ya kara talauta ’yan kasar wadanda da kyar suke iya biyan kudin makaranta da na asibiti da sauran bukatun su na yau da kullum.
Isa ya ce kawo yanzu gwamnatin ba ta kayyade matakan da za ta dauka ba domin rage radadin cire tallafin a kan masu karamin karfi .
Kazalika ya kara da cewa ba daidai ba ne Najeriya ta ci gaba da biyan tallafin da aka dade ana wawushewa ba kuma ya kamata gwamnati ta hukunta duk wani da aka samu da laifi a badakalar tallafin mai komai matsayin wanda aka kama da laifin.