Wata kotun masana’antu a Abuja ta sake jaddada hana ƙungiyar kwadago da ta manyan yan kasuwa tsunduma yajin aiki da ta yi a baya.

Alkalin kotun Justice Olufunke Aanuwe ne ya sake jaddada umarnin wanda ya bayar a ranar 5 ga watan Yunin da mu ke ciki.
Kotun ta ce dokar dakatar da tafiya yajin aikin da zanga-zanga ta na nan har sai an ci gaba da sauraron shari’ar.

Kotun ta sanya ranar Talata 20 ga watan Yuni domin sauraron ƙarar.

Gwamnatin tarayya ce ta shigar da korafi a kan shirin tafiya yajin aiki da kungiyar kwadago da kungiyar yan kasuwa su ka shirya tafiya bayan tashin farashin litar fetur.
Sai dai ƙungiyoyin sun janye tafiya yajin aikin bayan da su ka miƙa sharuda a gaban kwamitin gwamnatin tarayya kafin jayewa baki daya.
Farashin litar mai ya koma sama da naira 500 kan kowacce lita, wanda a baya ake siyarwa naira 185.