Rundunar ƴan sandan a jihar Jigawa sun kama wasu bindigu kirar gida gudaa uku da kuma wasu guda shida da ba a kammala ba.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Lawla Shiisu Adam ne ya bayyana haka a wata sanarwa daa ya rabawa manema labarai.

Haka kuma rundunar ta kwato wasu kayayyakin amfani da ake zargi sata ne.

Sannan yan sandan hadin gwiwa da jamian DSS sun kama wani Alassan Sabo Garba daa ake zargi shi ya ke hada makaman.

An kama shi a shagonsa da ke Garun Gabas a ƙaramar hukumar Malama Maadori ta jihar.

Hukumar ta ce su na ci gaba da bincike a kan gabanin gurfanar da wanda ake zargi a kotu don yi masa hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: