Gamayyar kungiyar cigaban Arewa maso Gabas (NEPC) ta bukaci da al’ummar Musulmi su yiwa mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima afuwa akan kalaman da yayi.

Kodinetan kungiyar Muhammad Konto Mafa shine ya bukaci haka, inda ya ce Shettima mutum ne mai nagarta musamman yadda ya nemi gafarar Musulmi akan nuna cancantar kirista akan musulmi.

Kungiyar ta bayyana cewa Shettima ya nemi afuwar Musulmi saboda haka ya cancanci a yi masa afuwa.

Mafa ya kara da cewa sakamakon dattako da kwarewa na iya shugabanci da Shettima ke dashi ne ya sanya ya nemi afuwar Musulmi.

Idan za a iya tunawa
Kashim Shettima a yayin wani taro ya bayyana goyon bayansa ga Kirista dan Kudu akan Musulmi dan Arewa mai nagarta a shugabancin majalisar dattawa ta 10 a Najeriya.

Bayan shettima yayi Kalaman hakan ya haifar da cece-cuke a tsakanin musulmi, inda su ke kalubalantar Kalaman na Shettima.

Leave a Reply

%d bloggers like this: