Gwamnatin jihar Zamfara ta musanta batun da ake cewa ta yi sulhu da yan bindigar Jihar.
Babban sakataren gwamnatin jihar ta Zamfara Abubakar Nakwada ne ya bayyana haka ga manema labarai a jiya Talata.
Ya ce gabadaya ma ba ya cikin niyar gwamna Dauda Lawal yin sulhu da yan bindiga a jihar.
Ya ce batun da ake cewa gwamnatin ta yi wani sulhu da yan bindiga a jihar a sirrance ba gaskiya ba ne.
Babu gudu babu ja da baya sannan gwamnati baza ta yi sulhu ba.
Ya ci gaba da cewa gwamnatin jihar Jihar Zamfara ta na ci gaba da aiki da sauran hukumomin tsaro na jihar domin yakin da dukkan yan ta’ada a jihar.
Abubakar Nakwada ya ce tsohuwar gwamnatin jihar ta Matawalle ta kashe akalla naira biliyoyin nairori don yaki da yan bindiga amma ba a san ina suka yi ba.
Sannan ya ce gwamnatin Zamfara zata bi dukanin hanyoyin da suka da ce don tabbatar da zaman lafiya a Jihar.
Daga karshe ya ce yakamata Alumma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro goyan Baya domin kara kaimi da yin aiki tare da Alumma bakidaya.


