Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bai wa jami’an tsaron kasar umaarni don ganin sun binciko tare da kama mutanen da ke kashe-kashe a jihar Filato.

Hakan na kunshe a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mau taimaka masa Dele Alake ya fitar ranar.

Matakin ya biyo bayan kashe-kashe da aka samu a ƙaramar hukumar Mangu a jihar wnada aka hallaka fulani sama da 70 a ranar Lahadi.

Kashe-kashen dai ya janyo gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita baki daya a karamar hukumar.

Haka kuma shugaban ya bayar da umarnin kawo karshen kashe-kashe a jihar Benue.

Ko a kauyen Farin Lamba n ajihar Filato an hallaka mutane ciki har da jaririya mai watanni Takwas.

Shugaba Tinubu ya ce wannan babban abin takaice ne.

Sannna ya bukaci gwamnatin jihar Filato ta da tabbatar ta ɗauki matakin gaggawa a kan waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Kuma shugaban ya bukaci kungiyar Jamaatu Nasrul Islam da ƙungiyar CAN da su haɗa kai don kawo karshen rikicin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: