Ma’aikatar ayyuka da gidaje a Najeriya ta ce matsalar tsaro ce ta sanya har yanzu ba a kammala aikin titin Abuja zuwa Kaduna da Kano ba.

Babban sakatare a ma’aikatar Alhaji Mahmuda Mamman ne ya bayyana haka yayin ganawarsa da ƴan jarida jim kadan bayan duba aikin.
Sai dai ya ce a wannan lokaci da aka samu cigaba a fannin tsaro aikin zai cigaba gadan-gadan.

Sannan ya sha alwashin kammala aikin nan da farkon shekarar 2024.

Sannan ma’aikatar ta gamsu da ingancin aikin da ake yi wanda ya bukaci ƴan kwangilar da su tabbatar sun kammala aikin a kan lokaci.
Tun a baya gwamnatin tarayya ta ce za ta kammala aikin kafin wa’adin mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
An fara aikin titin Abuja Kaduna zuwa Kano da nufin kammalawa cikin shekara biyu.